in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na damuwa da halin da 'yan matan da aka sace a Nigeria ke ciki
2014-05-08 14:30:16 cri

Wakiliya ta musamman a kan al'amurran yara kanana da tashe-tashen hankula a MDD, Leila Zerrougui ta shiga damuwa matuka, a sabili da makomar 'yan mata sama da 200, wadanda aka yi awon gaba da su daga makarantarsu dake arewa maso gabashin Nigeriya a watan Aprilu wannan shekarar.

Kakakin MDD Vannina Maestracci, ta ce, Zerrougui tare da sauran manyan jami'an MDD sun bukaci gwamnatin Nigeriya, da ta dauki matakan da suka dace wadanda za su tabbatar da 'yan matan sun dawo gida lafiya wajen iyalansu.

A game da kokarin da MDD ke wanzar wa a kan wannan lamari, kakakin MDD, Maestracci, ta ce, wakiliyar ta musamman ta ce, sakatare janar na MDD ya karfafa gwiwar kasashen duniya da su yi amfani da tasirinsu na ganin cewar, yaran da aka sace sun sami komawa ga iyalansu.

Wakiliyar ta musamman ta kuma ce, babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya yi gargadi a game da mugunta da ake amfani da ita a karin a hare-haren da ake kaiwa a arewacin Nigeria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China