Ma'aunin cinikayya na kasar Aljeriya ya samu wani gibi na dalar Amurka biliyan 8,041 a tsawon farkon watanni bakwai na shekarar 2015, idan aka kwatanta da na rarar kusan dalar Amurka biliyan 3,964 a makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, in ji kamfanin dillancin labarai na APS da ya rawaito sakamakon cibiyar kididdiga ta kasa (CNIS) dake aiki a karkashin hukumar kwastan ta kasar Aljeriya.
Da take ba da karin haske, majiyar ta tabbatar da cewa, daga watan Janairu zuwa karshen watan Yulin shekarar 2015, jimillar fitar da kayayyaki ta kai dalar Amurka biliyan 22,924 bisa ga dalar Amurka biliyan 38,49 na makamancin lokacin shekarar 2014, lamarin da ya nuna wata raguwa ta kashi 40.44 cikin 100. (Maman Ada)