Wasu rahotanni daga Algeria na cewa, dakarun sojin kasar sun hallaka mayakan wata kungiyar masu tada kayar baya mai alaka da Al-Qaida su 16.
Sojojin dai sun yi wa mayakan dirar mikiya ne a ranar Lahadi, a lardin Ain Defla mai nisan kilomita 145 daga kudancin birnin Algiers, fadar mulkin kasar.
Wannan mataki, a cewar wasu kafofin yada labarun kasar, ya biyo bayan farmakin da mayakan masu dauke da makamai suka kai wa wani rukunin sojojin kasar a ranar Juma'a, inda nan take suka hallaka sojoji 9, tare da jikkata wasu su 2.
Yayin harin daukar fansar da sojojin suka kai kaddamar a maboyar dakarun, sun hallaka 16 daga cikin su tare da kwato makamai da dama. (Saminu)