in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin Mali sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Algeria
2015-03-02 14:52:34 cri

Gwamnatin kasar Mali da kungiyoyin adawa guda shida daga arewacin kasar a ranar Lahadin nan suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a Algiers, babban birnin kasar Algeria domin kawo karshen zaman doya da manja da ke wanzuwa a yankin dake fuskantar tashin hankali.

Wannan yarjejeniyar zaman lafiyar, an samu nasara ta ne sakamakon zaman tattaunawa da aka yi har zagaye hudu tun daga watan Yulin bara karkashin shiga tsakanin kasar Algeria a madadin sauran kasashen da batun ya shafa.

Wani hadin gwiwwa tsakanin kungiyoyi uku da suka hada da kungiyar 'yantar da 'yan kasar kabilar Azawad, babbar hukumar hada kan Azawad da kuma kungiyar fafutukar Larabawan Azawad ba su rattaba hannu ba saboda sun bukaci karin tattaunawa da magoya bayansu daga tushe.

Sai dai kuma rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya ya samu jinjina daga kasar Algeria, Faransa da Amurka, har ma da kasashe makwabtan ita Mali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China