in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe kusan hamsin zasu aika tawagoginsu wajen bikin zantsar da shugaba Buhari
2015-05-23 17:13:59 cri
Kimanin kasashe hamsin ne a karkashin jagorancin shugabanninsu da ma wasu sauran tawagogi zasu halarci bikin rantsar da zababben shugaba Muhammadu Buhari, da aka tsaida shiryawa a ranar 29 ga watan Mayu a birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya, in ji ministan al'adu da yawon bude idon Najeriya, mista Edem Duke.

A yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja, mista Duke ya jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta isar da goron gayyata ga kasashen Afrika hamsin da hudu domin su halarci wannan biki. Kuma shugabannin kasashe da dama zasu halarci wannan bikin rantsar da shugaba Buhari har da na kasashen Turai, in ji mista Duke. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China