in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali da Algeriya sun tattauna kan hadin gwiwa da batun tsaro a Sahel
2015-02-11 09:59:28 cri

Firaministan kasar Mali Modibo Keita ya gana da shugaban kasar Algeriya Abdelaziz Bouteflika dangane da hadin gwiwwa, zaman lafiya a cikin kasar ta Mali, da kuma batun tsaro a yankin Sahel.

Modibo Keita ya bayyana wa manema labarai cewa, ya mika wa shugaba Bouteflika rubutaccen sako daga wajen shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita wanda ya shafi batun hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu, da kuma batun samar da zaman lafiya a cikin kasar ta Mali da nufin cimma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya.

A dangane da hakan, in ji firaministan na Mali, an zabi Algeriya ta jagoranci shiga tsakani daga bangaren kasashen duniya a kan batun sasantawa a cikin gidan Mali, inda ya ba da tabbacin cewa, zaman lafiya na samun ci gaba a hankali.

Yanzu haka, in ji Modibo Keita, wani sabon zaman tattaunawa a kan zaman lafiyar da aka fara a ranar Talatan wannan makon yana da zummar tattauna shirin mai zurfi domin cimma matsayar karshe. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China