in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da yarjejeniyar zaman lafiya a CAR
2015-05-12 10:31:18 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya yayin taron da aka yi a Bangui, yana mai cewa, hakan ya nuna kudurin al'ummar kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakaiya CAR wajen mai da tashin hankalin kasar ya zama tarihi.

Babban magatakardar MDD daga nan sai ya taya al'ummar kasar murna game da kudurin suna ganin sun samar da zaman lafiya ta amincewa da wannan yarjejeniya, sulhunta 'yan kasa baki daya, da kuma sake gina kasa a karshen taron Bangui din da aka yi a ranakun 4 zuwa 11 ga wannan watan.

A cikin wata sanarwa da kakakin majalissar ya fitar wa manema labarai, Mr Ban ya lura da cewa, kasar Afrikan ta Tsakiya ta yi fama da tashin hankali tun daga watan Maris na shekara ta 2013 lokacin da 'yan tawayen kasar musulmai karkashin kungiyar SELEKA suka karbi mulki, abin da ya kawo turjiya daga sauran sojojin sa kai mabiya addinin Kirista. An kafa gwamnatin rikon kwarya yanzu haka a kasar wadda aka dora wa alhakin ganin an shirya babban zabe cikin lumana tare da dawo da demokradiya mai karko.

Mr Ban daga nan sai ya yaba wa gwamnatin rikon kwarya da kuma kungiyoyi masu dauke da makamai a kan yadda suka amince da ajiye makamansu da sauran ka'idojin da aka fitar yayin taron Bangui.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China