in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da ministocin Zambia da Uganda
2015-01-07 09:46:38 cri

A jiya ne mamba a majalisar zartarwar kasar Sin Yang Jiechi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Zambia Harry Kalaba da karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Uganda Henry Oryem Okello a birnin Beijing na kasar Sin.

Yayin ganawar Yang ya ce, kasar Sin tana dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, kumar kasar Sin a shirye take ta taimaka wa kasahsen Afirka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inganta jin dadin jama'a da ci gaban tattalin arzikinsu.

Ya ce, kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen Afirka don bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za a samu sabon ci gaba.

Mr. Yang ya kuma tattauna da manyan jami'an kasashen na Zambia da Uganda kan batutuwan da suka shafi yin kwaskwarima ga kwamitin sulhu na MDD.

A nasu jawaban, ministocin kasashen na Zambia da Uganda sun bayyana cewa, kasar Sin sahihiyar kawa ce ga kasashen Afirka. Sun kuma gode wa kasar Sin bisa ga irin goyon bayan da take bayarwa kan harkokin kasa da kasa.

Daga karshe sun bayyana kudurinsu na kara inganta hadin gwiwa da musaya tsakanin su da kasar Sin a dukkan fannoni. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China