in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan Sinawan da suka rasu a sakamakon fashewar da ta auku a kasar Thailand ya kai mutum 7
2015-08-20 10:47:48 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Thailand, ya ce ya zuwa jiya Alhamis, yawan Sinawan da harin bam na kasar Thailand ya hallaka ya karu zuwa mutane 7, bayan da aka tabbatar da rasuwar mutum guda da a baya aka gaza sanin inda yake.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ya tabbatar da cewa, ya zuwa karfe 6 da dare na yammacin ranar Alhamis, Sinawa 7 sun mutu sakamakon harin na bom, ciki hadda mutane 5 daga babban yankin kasar, da kuma wasu mutum 2 daga yankin Hongkong.

Rahotanni sun nuna cewa bisa jimilla, harin bom din da aka kai a haikalin bauta na mabiya addinin Buddah ya halaka mutane 20, yayin da wasu 120 suka jikkata. Ban da Sinawa 7 da suka rasa rayukansu, saura mamatan sun fito ne daga kasashen Thailand, da Singapore, da Malaysia da dai sauran kasashe.

Firaministan kasar Thailand Prayuth Chan-ocha ya ce, wannan ne hadari irin sa mafi muni da Thailand ta taba gamuwa da shi a tarihin ta.

An ce, yanzu haka 'yan sandan kasar ta Thailand na ci gaba da bincike kan lamarin, tare da tayin lada na makudan kudade, ga duk wanda ya gabatar da gamsassun bayanai, da za su bada damar cafke wanda ya kaddamar da wannan hari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China