in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Thailand ta rushe majalisar wakilan kasar.
2013-12-10 16:07:06 cri
Firaministan kasar Thailand Yingluck Shinawatra ta sanar da rushe majalisar wakilan kasar a ranar Litinin 9 ga watan nan, inda a yanzu haka gwamnatin kasar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa watan Fabrairun shekara mai zuwa, lokacin da za a gudanar da babban zaben kasar.

Da safiyar wannan rana ne dai Ms. Shinawatra ta sanar da rushe majalisar tana mai cewa gwamnatin ta, ta tsai da kudurin rushe majalisar wakilan ne, don mika ikon ta ga jama'ar kasa, ta yadda za a gudanar da babban zaben kasar mai zuwa karkashin tsarin dimokuradiyya.

Haka zalika a daren wannan rana, shugaban kungiyar 'yan adawa da gwamnatin kasar Suthep Thuagsuban, ya yi kira ga magoya bayan sa da su ci gaba da yin gangami, don nuna bukatar saukar firaministan mai ci daga mukaminta.

A nasa bangare kakakin jam'iyyar dake mulkin kasar Thailand ta Pheu Thai Party, ya bayyana cewa manyan jami'an jam'iyyar sun cimma ra'ayi daya, na maida Yingluck Shinawatra matsayin babbar 'yar takara yayin babban zaben kasar dake tafe a shekara mai zuwa, kuma ana sa ran ta ci gaba da kasancewa babbar 'yar takarar jam'iyyar yayin taron jam'iyyar da za a yi a ranar 11 ga wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China