in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala zabe a kasar Thailand
2014-02-03 16:49:59 cri
Rahotanni daga kasar Thailand na cewa, da karfe 3 na yammacin ranar Lahadi agogon kasar ne aka kammala babban zaben kasar mai cike da rudani.

Duk da cewa, an fara kidaya kuri'u, amma ba za a samu sakamakon zaben a ranar Lahadi ba, sai bayan an gabatar wa hukumar zaben kasar da sakamakon zaben tare da kammala zabuka a wuraren da tun farko aka hana gudanar da zaben a wasu tashoshin zaben kasar.

Rahotanni daga kafofi watsa labaran kasar na cewa, kimanin mutane miliyan 12 cikin mutane miliyan 48.77 da suka cancanci yin zabe a kasar, ba su fito zaben na ranar Lahadi ba, sakamakon toshe tashoshin zabensu da masu adawa da gwamnati suka yi da kuma wasu mazabu 28 da ba su tsayar da 'yan takara a babban zaben kasar ba.

An tsayar da ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaben cike gurbi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China