in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Thailand Yingluck Shinawatra ta sanar da rushe majalisar wakilan kasar
2013-12-09 16:35:34 cri

A ran 9 ga wata da safe ne, firaministar kasar Thailand Madam Yingluck Shinawatra ta yi wani jawabi a gidan talibijin din kasar, inda ta sanar da rushe majalisar wakilan kasar, haka kuma ta yi nuni cewa, za ta tsayar da lokacin sake yin babban zabe ba tare da bata lokaci ba, a cikin wannan wa'adi, firaministar da majalisar ministoci za su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

An kasa majalisun kasar Thailand zuwa sassa biyu wato majalisar dattawa da majalisar wakilai, sarakuna ne suke nada wasu mambobin majalisar dattawa, wadda ba a rushe ba yanzu.

Wannan ranar ta zama yaki na karshe da shugaban 'yan adawa da gwamnati da ke tarurruka Mista Suthep Thuagsuban, a halin yanzu masu zanga-zanga sun fara tarurruka,inda suka fara yin tattaki zuwa fadar firaministar. Wasu muhimman mutane da ke halartar tarurrukan sun ce, ba za su gamsu da rushe majalisar dokoki ko korar firaministar ba, za su ci gaba da shirinsu na da, wato na kafa wata majalisar jama'a.

A ran 9 ga wata, kungiyar da ke adawa da gwamnati ta Thailand wato kwamitin yin gyare-gyare don samar tsarin dimokuradiyya ga jama'a ya bukaci firaministar wucin gadi Madam Yingluck da mambobin majalisar ministocinta su sauka daga mukamansu, don share fage ga kafuwar majalisar jama'a.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China