130617VOICE-DRUGS-IN-KANO-bagwai
|
Daga cikin magungunan da aka kona sun hada da na Tari, da na kashe kwayoyin cuta da magungunan ciwon ido da ciwon kunne da mayikan shafawa a kuraje da allurai da kuma wasu lemukan sha wadanda wa`adin aikin su ya kare.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da gwamnan jihar Kano Injniya Rabi `u Musa Kwankwaso ya jagoranci kone jabun magunguna da sauran kayan abinci da wa`adin amfani da su ya kare, tun bayan kasancewarsa gwamna a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu gwamnatin Kano ta lalata irin wadannan kayayyaki da kudinsu ya kai sama da naira buliyan biyu.
Da yake jawabi bayan an cinnawa magungunan wuta, Gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso ya ce abun takaici duk da kokarin da gwamnatinsa ke yi na dakile cinikin jabun magunguna a jihar, amma sai ga shi wasu batagari suna bin haramtattun hanyoyin shigo da irin wadannan magunguna ba tare da tunanin illolin dake tattare da yin hakan ba ga yanayin lafiyar al`umma.