in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manajan kamfanin jiragen saman Sin na China Southern: za mu kafa wata gada a sama don hada kasar Sin da kasashen Afrika
2015-08-05 13:48:10 cri

A safiyar Larabar nan ne 5 ga wata, kamfanin jiragen saman kasar Sin na China Southern, ya kaddamar da aikin sufuri zuwa nahiyar Afrika. Duk da cewa, Sin da Afrika na da matukar nisa, amma idan akwai jiragen sama kai tsaye a tsakaninsu, hakan zai kawo sauki duk kuwa da tarin kalubalen da wannan aiki zai iya fuskanta.

Yayin da shugaban kamfanin jiragen sama na China Southern Si Xianmin ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana halin da ake ciki game da shirin layukan da kamfaninsa zai bi zuwa nahiyar Afrika. Ya ce, sabon layin zirga-zirgar sama tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zai hada birnin Guangzhou na kasar Sin da birnin Nairobi na kasar Kenya, kuma jirgin sama kirar Airbus A330 zai rika daukar fasinjoji sau 3 a ko wane mako a kan wannan hanya.

Tun dai cikin watan Yuni na shekarar 2014, kamfanin ya kaddamar da layin nasa daga birnin Shenzhen zuwa Mauritius. Bayan da aka gudanar da wannan layin jiragen sama har na tsawon shekara guda, jiragen sama na China Southern sun yi kai-komo tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika har sau 146, kuma sun dauki fasinjoji kimanin dubu 26. Kana an kara yawan sawayen sufuri daga sau daya a ko wane mako na da zuwa sau biyu a ko wane mako a yanzu. Bugu da kari, kamfanin China Southern na tattaunawa kan yiyuwar kara sawayen sufurin zuwa sau 3 a ko wane mako.

A watan Disambar shekarar 2006, a yayin taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kamfanin ya taba bude layin jiragen sama na farko zuwa nahiyar Afrika wanda ke tashi daga Beijing, kuma ya tsaya a birnin Dubai sannan ya isa birnin Lagos na Najeriya, kuma an gudanar da wannan sufuri ne sau 3 a ko wane mako. Daga bisani kuma, sakamakon rikicin kudi na duniya, da tangal-tangal na farashin man fetur, wannan layi ya samu hasarar kudade kimanin miliyan 400 cikin shekaru 3, lamarin da ya sa a dage wannan layi a shekarar 2009.

Mr. Si ya ce, bude layin jiragen sama tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, ya kasance wani babban nauyin da gwamnatin kasar ke baiwa kamfanonin jiragen sama, kuma idan ana son cimma burin hada kasar Sin da kasashen duniya baki daya, ya kamata a cimma wannan burin. Akwai babbar dama da kalubale sosai a kasuwar kasashen Afrika, kamfanin China Southern yana fatan taka rawar a zo a gani a fannin sha'anin hada kasar Sin da kasashen Afrika.

Ya ce, batun dakatar da layin jiragen sama zuwa birnin Lagos ya bai wa kamfaninsa wani muhimmin darasi, wato idan babu karfi sosai, babu kuma abokan hulda masu kyau, shiga cikin kasuwannin kasashen waje ba zai dace da ka'idar raya kamfanin ba.

A cikin shekaru 6 da suka wuce, tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin ya samu habaka sosai, kuma kamfanin China Southern shi ma ya samu babban ci gaba, baya ga dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta shiga sabon mataki. Haka zakila, gwamnatin Sin ta gabatar da shirin kafa gamayyar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, da shirin hadin gwiwa a fannin zirga-zirgar sama tsakanin bangarorin biyu. A cewar Mr. Si, duk wadannan sun bai wa kamfaninsa babbar dama wajen shiga kasuwar kasashen Afirka.

Si Xianmin ya ce, kamfanin jiragen saman fasinja ya zama wani kamfanin ba da hidimomi ga jama'a, duk da cewa, kamfanin ya tsara dabaru bisa manyan tsare-tsare sosai, amma bai kamata a manta da babban tushen kamfanin ba, wato batun ba da hidima ga jama'a. Don tabbatar da gudanar wannan layi a tsakanin Guangzhou zuwa Narobi yadda ya kamata, bayan da kamfanin ya samu izinin gudanar da wannan layi a watan Maris na bana, kamfanin ya tura rukunin bincike da rukunin yada bayanai ga kasar Kenya, don bude kasuwannin kasar tun da wuri, da kara sanin yanayin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da al'adu da bukatu a kasuwannin kasar.

Si Xianmin ya ce, kasancewar layin jiragen saman a matsayin wata gada, bai kamata a yada bayanai game da hakan a hannu guda kawai ba, shi ya sa kamfanin ya shirya bukukuwan yada bayanai game da layin a birane 12 na kasar Sin, cikinsu har da Beijing, da Shanghai, da Chengdu da Wuhan da dai sauransu, baya ga wasu birane na kasashen Kenya, Uganda da kuma Tanzania. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China