Bayan kammala wani taro a ranar Talata a birnin Conakry, hedkwatar kasar Guinea, shugabannin manyan jam'iyyun adawa na kasar sun cimma wata yarjejeniya domin ganin 'yan adawa su halarci taron shawarwarin siyasa da aka tsaida shirya wa a wannan ranar Alhamis.
Yan adawa na da niyyar tura wata tawagar takaitattun mutane a yayin wadannan shawarwari, inda za'a tattauna mahimman batutuwan da suka shafi harkokin shirya zabuka, in ji kakakin kawacen adawan kasar Guinea, Aboubacar Sylla bayan fitowarsa daga wannan taro. (Maman Ada)