Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a ranar Litinin da yamma a Memorom, wani kauyen da ke gabar tafkin Chadi, tare da kashe da mazauna wurin da kona gidajensu, a cewar kafofin yada labarun kasar Chadi a ranar Laraba.
An kai harin a lokacin da mutanen ke bude baki na azumin watan Ramadan. Majiyoyin wurin da kafofin yada labarai suka rawaito, sun tabbatar da cewa mutane 18 suka mutu.
Gwamnan yankin tafkin, Kedallah Younous Hamidi, da ya kai ziyara wurin da aka kai harin, a nasa bangare ya bayyana cewa, mutane uku suka mutu, yayin da mutane kusan goma suka jikkata.
Mista Younous Hamidi ya bayyana harin da wata ramuwar gayya da daukar fansa na 'yan ta'addan kan 'yan uwansu da suke watsi da irin tunaninsu ko kuma suka amincewa su bi su.
Wadannan mayakan Boko Haram, da suka rarrabu zuwa kananan gungun mutane 10 zuwa 20 bayan jami'an tsaron kasar Chadi suka karya lagonsu, na kokarin hada kansu domin kai hare hare kan wadannan kauyuka, in ji jami'in.
A ranar 6 ga watan Afrilu, mayakan Boko Haram suka kashe wasu kauyawa guda bakwai, da suka dawo daga kasuwa, bayan sun yi musu kwanton bauna kusa da kauyensu.
Wadanda suka aikata wadannan hare hare, mutane ne na kusa da kauyukan da ke wannan yanki. Akwai hannun wasu da dama daga cikin wadannan hare hare, in ji gwamnan Tafkin. (Maman Ada)