in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya kara wa'adin UNSOM da ke Somaliya
2015-07-29 09:34:35 cri

A jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri'ar bai daya ta kara amincewa da wa'adin tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya wato UNSOM a takaice.

Bugu da kari, kwamitin ya sake amincewa da kara wa'adin dakarun kungiyar tarayyar Afirka (AMISOM) da ke aiki a kasar ta Somaliya har zuwa ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2016.

Shawarar da mambobin kwamitin sulhun suka yanke game da karin wa'adin tawagar ta UNSOM zuwa ranar 30 ga watan Maris din shekarar 2016 ta zo ne bayan da mayakan Al-Shabaab suka kaddamar da wani mummunan hari kan wani otel a birnin Mogadishu na kasar ta Somaliya. Harin da ya halaka mutane da dama, ciki har da mai aikin gadi a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Somaliya.

Daga bisani kungiyar Al-Shabaab mai alaka da kungiyar al-Qaida dai ta dauki alhakin kai harin a matsayin mayar da martani ga hare-haren baya-bayan nan da dakarun kungiyar AU da sojojin Somaliya suka kaddamar a yankunan Dinsoor da Bardhere da ke kudancin Somaliya.

Wannan kudurin da kwamitin sulhun ya kada ya nuna yadda MDD ke mutunta 'yancin kasa da na siyasa da kuma hadin kan kasar ta Somaliya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China