in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya kara wa'adin aikin zaman lafiya a Somaliya
2015-05-27 09:49:32 cri

Kwamitin tsaro na MDD a ranar Talatan nan ya kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya UNSOM zuwa watan Agusta, ganin yadda kasar ke kokarin farfadowa daga turban siyasa da tsaurara tsaro.

Sabon wa'adin da kwamitin tsaron ya amince da shi yanzu zai kare a ranar 7 ga watan Agusta.

Amincewar daga kwamitin mai mambobi 15 ta mutunta ikon kasar Somaliya da 'yancin siyasarta, ikon yankinta, da kuma hadin kanta, sannan ta ba da dama ga MDD da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU su sake duba ayyukan AU a kasar.

Sannan kuma kwamitin ya sake nanata kiran shi ga MDD da AU da su ba da sabbin shawarwari na matakan da za'a dauka na soji a kan Al-Shabaab, kungiyar masu tsatsauran ra'ayi da ta kaddamar da yaki tsakanin ta da gwamnatin Somaliya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China