in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun ci gaba a Somaliya, in ji wakilin MDD
2015-05-20 10:29:33 cri

Wakilin babban magatakardar MDD a Somaliya Nicholas Kay, ya ce, ana samun ci gaba sannu a hankali a kasar, duk kuwa da kalubalen da mayakan kungiyar Al-Shabaab ke haifarwa. Kay ya ce, akwai tarin nasarori da Somaliya ta samu a fannin gudanar da mulki, ko da yake lokaci bai yi ba, da za a fara murnar nasarorin da kasar ke samu.

Kaza lika wakilin na MDD wanda ya yi wa taron kwamitin tsaron majalissar karin haske game da rahoton baya bayan nan, na babban magatakardar MDDr game da halin da ake ciki a kasar ta kafar talabijin, ya ce, lokaci ya yi da kasashen duniya da su mai da hankali, ga irin nasarar da aka samu a Somaliya, musamman ma a fannin shawarwarin siyasa, da yunkurin dakile ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

Ya ce, daya daga hanyoyin da suka dace a mai da hankali a kan su a fannin tsaro shi ne, tabbatar da katse damar kungiyar Al-shabaab ta samu tallafi daga kungiyoyin kawance dake kasar Yemen.

Duk dai da wannan ci gaba da ake samu a Somaliya, wasu rahotanni na nuna cewa, halin jin kai na da tsananta a kasar, duba da yadda kusan mutane 730,000 ke ci gaba da fuskantar matsalar karancin abinci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China