in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi tir da hari kan jami'an diflomasiyya a Somaliya
2015-06-26 10:02:07 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai, da wani harin bam da aka kai kan tawagar jami'an aikin jin kai 'yan hadaddiyar daular Larabawa a Somalia. Harin da ya hallaka mutane 14, ciki hadda sojojin Somaliya su 4 dake rakiyar jami'an.

Rahotanni sun ce, an kaddamar da wannan hari ne a birnin Mogadishu a Laraban da ta gabata, ko da yake dai jami'an 'yan hadaddiyar daular Larabawa sun tsiri daga harin.

Wata sanarwa da kwamitin tsaron ya fitar bayan aukuwar wannan lamari, ta bayyana sakon ta'aziyya ga iyalai, da 'yan uwan wadanda wannan hari ya ritsa da su, da kuma gwamnatocin kasashen su.

Sanarwar ta kuma yi kakkausan suka ga wannan ta'asa, wadda ka iya dakile nasarar ayyukan jin kai, wadda wakilan kasashe daban daban ke gudanarwa a Somaliya, baya ga yiwuwar hallaka fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Kaza lika sanarwar ta bayyana hare-haren ta'addanci a matsayin mummunan aiki maras dalili, ko da kuwa wane ne ya dauki nauyin aikata shi.

Daga nan sai kwamitin ya bukaci da a gaggauta kame, tare da gurfanar da masu hannu cikin wannan lamari gaban kuliya domin fuskantar shari'a. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China