in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya da Nijar na goyon bayan shirin Nouakchott a yankin Sahel
2015-01-28 10:29:56 cri

Kasashen Aljeriya da Nijar sun jaddada a ranar Talata a birnin Alger goyon bayansu kan shirin Nouakchott na zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel, musammun a kasashen Mali da Libiya, a cewar wata sanarwar da ta biyo bayan ziyarar aiki ta kwanaki uku da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kai a kasar Aljeriya.

Sanarwar hadin gwiwar ta jaddada cewa, shugabannin kasashen Aljeriya da Nijar sun nuna yabo kan makomar dangantakar dake samun ci gaba, da ma karfafa a fannin tsaro a shiyyarsu, tare da nuna goyon bayansu kan shirin Nouakchott dake manufar aiwatar da tsarin zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel.

Shirin Nouakchott da kungiyar tarayyar Afrika ta kaddamar a cikin watan Maris din shekarar 2013, na da manufar karfafa dangantakar tsaro da musanyar bayanai a yankin Sahel. Kasashe goma sha daya sun kunshi wannan shirin, wadanda suka hada da Aljeriya, Burkina-Faso, Cote d'Ivoire, Guinea, Libiya, Mali, Mauritaniya, Nijar, Najeriya, Senegal da Chadi.

Da suke tabo magana kan kasar Libiya, shugabannin kasashen biyu, sun bayyana damuwarsu kan matsalar da Libiya ke fuskanta, dake kasancewa wata barazana ga al'ummar kasar, da ma shiyyar baki daya. Domin magance wannan matsala, shugabannin kasashen biyu, sun jaddada wajabcin girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Libiya, tare da ba da kwarin gwiwa wajen yin shawarwari tsakanin bangarori masu gaba da juna a kasar Libiya da manzon musammun na sakatare janar na MDD game da kasar Libiya, Bernardino Leon ya kaddamar domin kai ga cimma wata mafitar siyasa da za ta tabbatar da hadin kan kasa, cikakken yankin kasa, zaman lafiya da zaman jituwa tsakanin al'ummar Libiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China