in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da shirin samar da agaji a Yemen
2015-07-27 09:32:00 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da sanarwar da dakarun da kasar Saudiya ke jagoranta ta bayar na dakatar da hare-haren da suke kaiwa a kasar Yemen na tsawon kwanaki biyar, ta yadda za a samu nasarar kai kayan agaji ga fararen hula.

Wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa, Ban ya bukaci mayakan Houthi da sauran sassan da abin ya shafa, da su martaba shirin samar da agajin don kare muradun 'yan kasar Yemen.

Bugu da kari, Ban Ki-moon ya yi kira ga dukkan bangarorin da rikicin kasar ta Yemen ya shafa, da su dakatar da hare-haren da suke kaiwa a lokacin da ake gudanar da shirin samar da agajin, don ganin an isar da kayayyakin jin kai, ciki har da magunguna ga mutanen da ke matukar bukata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China