in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bam ya hallaka mutane 8 a birnin Sanaa na Yemen
2015-07-21 09:43:01 cri

Rahotanni daga birnin Sanaa, fadar mulkin kasar Yemen na cewa, wani bam da mayakan kungiyar IS suka dana jikin wata mota ya hallaka Abdul Karim al-Kuhlani, wanda kusa ne a kungiyar Houthi ta 'yan Shi'a da wasu mutane 7 dake tare da shi.

Wani jami'in tsaron birnin da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana wa majiyarmu cewa, harin bam din wanda ya tarwatsa jerin gwanon motocin Al-Kuhlani, ya auku ne da yammacin jiya Litinin a unguwar Al-Jeraf dake arewacin birnin Sanaa. Ya ce, baya ga wadanda suka rasu yayin harin, akwai kuma wasu da dama da suka samu raunuka.

Wani ganau mai suna Hashim al-Zain, ya shaida wa majiyarmu cewa, sun yi mamakin yadda wannan hari ya auku a bayan wani masallaci dake unguwar Al-Jeraf, kuma sun yi matukar Allah wadai da aukuwar hakan.

Mayakan kungiyar IS dai sun dauki alhakin kaddamar da harinta cikin wata sanarwa da suka sanya a shafin Twitter, suna masu cewa, harin daya ne daga matakan ramuwar gayya da suke dauka, bisa kisan fararen hula da mayakan 'yan shi'a ke aikatawa a kasar.

Wannan hari dai shi ne irinsa na 5 da IS ta kaddamar kan 'yan shi'ar Houthi, tun harin farko da aka kai musu cikin watan Yunin da ya gabata a birnin na Sanaa.

Yanayin tsaro dai na kara tabarbarewa a Yemen, tun bayan boren shekarar 2011, wanda ya yi awon gaba da shugaban Ali Abdullash Saleh. Kaza lika matakan tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da nufin sulhuntawa sun ci tura, matakin da ya haifar da kafuwar kungiyoyin tada kayar baya kamar Al-Qaida da IS a kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China