in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta dauki niyyar karfafa harkokin kudi na shiyyar
2015-07-24 12:54:41 cri

Gamayyar ci gaban kasashen SADC, ta bude wani zaman taro (Indaba) a ranar Alhamis kan batun shigo da harkokin kudi a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, inda ta yi alkawarin kara karfafa shigo da harkokin kudi na shiyyar.

Duk da cewa an samu ci gaba, babban adadi na rashin amincewa a cikin harkokin kudi na ci gaba da karuwa sosai a cikin kasashe mambobin kungiyar SADC, in ji ministan kudin Afrika ta Kudu Nhlanhla Nene a cikin jawabinsa na bude taron.

Shigo da harkokin kudi wata hanya ce ta samun kudi da yin amfani yadda ya kamata da hukumomin kudi ta fannonin harkokin kudi da jama'a suka daidaita, inda hukumomin kudi suke da muhimminci, ko da yake har yanzu ba su isa sosai ba yadda ya kamata.

Shigo da harkokin kudi masu gatanci, wani mihimmin mataki ne bisa ajandar ci gaban shiyyarmu, haka kuma shigo da harkokin kudi na kasancewa wani muhimmin abin dole ga ci gaba, in ji mista Nene.

A cikin shekarun baya baya, kasashe da dama na shiyyar sun aiwatar da sauye sauye masu mihimmanci domin gina wani tattalin arzikin, inda a ciki dukkan mutane na iya halarta yadda ya kamata, kuma su samu alfanu, tare da ci gaban da aka samu a shirin gina wata al'umma mafi adalci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China