in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC na nuna damuwa kan rikicin Lesotho
2015-07-07 10:41:53 cri

Kungiyar tattalin arzikin kasashen dake kudancin Afrika ta SADC na ci gaba da nuna damuwa kan rikicin Lesotho, in ji shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a ranar Litinin.

An gudanar da taron ministoci da dama tare da shirya tarukan gaggawa domin tattauna matsalar da bullo da hanyoyin warware wannan rikici ta hanyar zaman lafiya da karko, in ji mista Zuma a yayin dandalin 'yan majalisun kungiyar SADC da ke gudana a Zimbali, gundumar KwaZulu-Natal.

Ya ce, tagwayen tarukan shugabannin SADC, da aka shirya a birnin Pretoria a makon da ya gabata, sun taimaka wajen tura wata tawagar sanya ido ta kungiyar SADC zuwa Lesotho, baya ga kuma mai shiga tsakani na kungiyar SADC wato mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China