in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin SADC zai koma Lesotho don aikin shiga tsakani
2015-03-05 10:42:45 cri

Mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa a matsayin shi na wakilin kungiyar raya kudancin Afrika SADC zai koma Lesotho domin ci gaba da aikin shiga tsakani, kamar yadda aka sanar a ranar Laraba.

Wannan ziyarar da zai kai tsakanin ranar 4 da 5 ga watan na Maris ta biyo bayan zaben da aka kammala ba da dadewa ba wanda kungiyar ta SADC ta gabatar, in ji kakakin Mr. Ramaphosa, Ronnie Mamoepa.

Al'ummar kasar Lesotho sun yi saurin kada kuri'unsu a ranar Asabar din da ta gabata domin kawo karshen rikicin siyasa da ya addabi kasar, abin da ya kamata sai nan da shekaru biyu za'a gudanar bisa ga yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar SADC.

Kungiyoyin sa ido da suka lura da zaben sun bayyana shi da gudana cikin adalci, kuma a bayyane kamar yadda kungiyar AU da EISA na kasashen Ingila suka tabbatar.

Sakamakon farko ya nuna cewa, jam'iyyar firaministan yanzu Thomas Thabane, ABC ce ke kan gaba. Ana sa ran cikakken sakamako a yau Alhamis, wanda Ramaphosa zai sa ido a kai. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China