Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke jamhuriyar demokiradiyar Congo DRC (MONUSCO), ta tabbatar da cewa, ta kai hari kan 'yan tawayen da aka bayar da rahoton cewa, sun halaka a kalla fararen hula 42 a gabashin lardin Arewacin Kivu.
Tawagar ta MONUSCO ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta bayar ranar Alhamis, tana mai cewa, jiragenta masu saukar ungulu sun yiwa 'yan tawayen Uganda na ADF-NALU kawanya ranar Laraba, inda suka sake kwace yankunan da ke hannun 'yan tawayen da ake zargi da halaka fararen hula 42 a kauyen Kamango da ke kan iyaka da kasar Uganda.
Shugaban wata kungiyar fararen hula a Arewacin Kivu Mwiti Thomas, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ta wayar tarho cewa, 'yan tawayen na ADF-NALU, sun samu nasarar halaka mutanen ne tare da tallafin 'yan tawayen M23, lokacin da dakarun jamhuriyar demomiradaiyar Congo suka kaddamar da wani hari kan yankunan Kamango da 'yan tawayen suka kwace.
A wani labarin kuma, hukumomin tsaro a Arewacin Kivu, sun shaidawa Xinhua cewa, a ranar Alhamis dakarun kasar ta Congo ( FARDC) sun kaddamar da wani mummunan hari kan 'yan tawayen ADF-NALU a kusa da Kamango. Wasu majiyoyin MDD na bayyana cewa, an kashe a kalla 'yan tawaye guda 10, kana ma'aikatan wanzar da zaman lafiya da dama sun jikkata a fadan.
Bayanai na nuna cewa, wannan lamari ya dakushe fatan da ake shi na farfadowa daga shekara da shekaru da aka kwashe ana fama da matsalar 'yan tawaye, bayan da gwamnatin Congo da babbar kungiyar 'yan tawaye ta M23 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a farkon wannan wata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. (Ibrahim)