in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na shirin kafa guraben ayyukan yi miliyan 1.2 tare da taimakon internet
2015-07-22 10:19:52 cri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa, ta bullo da wani shirin kafa guraben ayyukan yi ga matasan kasar tare da taimakon harkokin internet, da ma sauran ayyukan da suka jibanci wannan fanni.

Babban darekta cibiyar bunkasa harkokin kimiyya da fasaha ta kasa, Peter Jack ne ya yi wannan sanarwa a yayin wani dandali a birnin Abuja, hedkwatar kasar, tare bayyana cewa, cibiyarsa na shirin bullo da damammaki domin baiwa matasa masu gudanar da sabbin kamfanoni damar kulawa da harkokin tattalin arzikinsu.

Muna shirin kafa dangantaka tare da bankin bunkasa masana'antu, babban bankin Najeriya, kuma muna aiki tare da wasu ma'aikatu a wannan fanni, muna shirin fara aiki da tsarin E-government a bangaren gwamnonin cikin gida, jihohi da na tarayya, in ji wannan jami'in.

Mista Jack ya kara bayyana cewa, ma'aikatarsa na shirin kuma horar da ma'aikatan gwamnati a dukkan fadin kasar, tare da jaddada cewa, fasahar internet na da muhimmanci sosai domin baiwa matasan Najeriya damar kafa masana'antunsu, da tabbatar da 'yancinsu na tafiyar da harkokinsu.

Kwararrun da suka halarci wannan dandali sun jaddada muhimmancin internet ga matasa domin internet ya zama wani babban tushe ga zama wani shugaban kamfani.

Najeriya na da yawan matasa kimanin miliyan 80, wadanda daga cikinsu kashi 64 bisa dari ba su da ayyukan yi, in ji kwararrun, tare da nuna cewa, babu bukatar dole cewa sai su yi aiki a hukumomin gwamnati. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China