in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta cafke mutumin da ya shirya hare haren baya baya nan
2015-07-09 10:49:26 cri

Kasar Nijeriya ta bayyana a ranar Laraba cewa, ta kama mutumin da ya shirya jerin hare haren kunar bakin wake a cikin kasar, kusa da wata tashar bincike da ke arewacin kasar.

Mutumin da ake zargi, da ba a ba da sunansa ba, an kama shi a jihar Gombe dake arewacin kasar, tare da wasu mutane biyu, a lokacin da suke kokarin tserewa binciken tsaro, a cewar wata sanarwar da kakakin rundunar sojojin Najeriya, kanal Sani Kukasheka Usman ya sanya wa hannu.

Kusar shirya hare haren ta'addancin da abokansa biyu sun yi kokarin tserewa binciken tsaro, amma sojojin Najeriya suka kamo su. A halin yanzu, 'yan ta'addan da aka kama za su bayyana gaban kotu, kuma doka za ta yi aikinta, in ji wannan sanarwa.

Wannan mutumin, ana zargin sa da shirya hare haren ranar Lahadi a birnin Jos, hedkwatar jihar Filato dake tsakiyar Najeriya, da na ranar Litinin a birnin Zaria dake jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar. Hare haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 73, tare da jikkata mutane da dama.

Dalilin haka ne, sojojin Najeriya tare da 'yan sanda masu farin kaya suka kafa wani shingen bincike a cikin wadannan yankuna, musammun ma kusa da wuraren da aka kai hare haren. Kuma wannan kangiya ta taimaka wajen kama mutumin da ya shirya wadannan munanan hare hare tare da mutanensa biyu, in ji sanarwar rundunar sojojin Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China