Wata majiyar tsaro a Najeriya ta tabbatar da mutuwar a kalla mutum guda, kana wasu mutane uku suka jikkata, bayan da wani 'dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ke jikinsa a wata tashar binciken ababan hawa a kusa da garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno
Wani jami'in tsaro da ya bukaci a sakaye sunansa, ya bayyana cewa, 'dan kunar bakin waken da ke cikin wata motar bas ya tarwatsa kansa ne, bayan da fasinjojin da ke cikin motar suka fita daga cikin motar domin jami'an tsaro su bincike su kamar yadda aka saba.
Bugu da kari, fashewar ta jikkata wasu ma'aikatan 'yan kungiyar nan ta kato da goro da ke taimakawa jami'an tsaro a jihar ta Borno da ke fama da tashin hankali, wadanda daga bisani aka garzaya da su zuwa babban asibitin Umaru Shehu da ke garin na Maiduguri don yi musu magani. (Ibrahim)