in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce yawan 'yan gudun hijira ya karu a watanni 6 na farkon shekarar 2014
2015-01-08 10:15:29 cri

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, adadin al'ummun da tashe-tashen hankula suka raba da gidajen su a bara, ya haura adadin da ake taba samu a baya.

Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labaru, ya ce, yake-yake a yankunan Gabas ta Tsakiya, da nahiyar Afirka, sun raba kimanin mutanen miliyan biyar da rabi da gidajen su, cikin watannin 6 kacal a shekarar ta bara.

Mai magana da yawun MDDr ya kara da cewa, kasar Sham ce ke kan gaba a kasashen da suka fi yawan 'yan gudun hijira.

Da yake karin haske game da adadin 'yan gudun hijirar da hukumar UNHCR ta fitar a 'yan kwanakin baya, Dujarric ya ce, cikin mutane miliyan 5 da rabi da suka gujewa muhallan su, miliyan 1 da 400,000 sun fice daga kasashen su na haihuwa, yayin da sauran ke samun mafaka a wasu yankunan dake cikin kasashen nasu.

Kaza lika sabbin alkaluman sun shaida cewa, ya zuwa tsakiyar shekarar baran, hukumar MDDr mai lura da 'yan gudun hijira ko UNHCR, ta ba da tallafi ga kusan mutane miliyan 46 da 300,000. Adadin da ya haura na karshen shekarar 2013 da karin kusan mutane miliyan 3 da 400,000. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China