Rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa, za a samar wa sabuwar cibiyar yaki da mayakan Boko Haram (MCCC) da aka girke a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar da ke fama da hare-haren Boko Haram kayan aiki na zamani, ta yadda za ta fuskanci yakin da take yi da mayakan Boko Haram.
Kakakin sojojin kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai. Ya ce, daga yanzu cibiyar ce za ta rika tsara dabaru da samar da muhimman bayanai da za su kai ga nasarar kakkabe mayakan na Boko Haram baki daya.
Bugu da kari, cibiyar ta MCCC ce za ta rika musayar muhimman bayanai tsakanin sojojin Najeriya da kuma dakarun hadin gwiwar da za a tura yankin tafkin Chadi a karshen watan Yulin wannan shekara.
Idan ba a manta ba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin mayar da cibiyar yaki da mayakan na Boko Haram daga Abuja zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno a lokacin jawabinsa na rantsuwar kama aiki.(Ibrahim)