Shugaba Xi ya kara da cewa, a karkashin kokarin bangarorin biyu, yanzu haka ana daukar matakai na cimma matsaya guda da aka daddale tsakaninsu, kana kasashen biyu na inganta hadin gwiwa a fannonin kafa dokoki, da gina hanyoyin jiragen kasa da masana'antu na sana'o'i, da sauran fannoni.
A nasa bangare, firaminista Modi ya ce India na maraba da masana'antun Sin a fannin zuba jari a kasar India. Kana kasarsa na sa ran inganta tuntubar juna da shawarwari bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, don daidaita sabani game da shata iyakokin kasashen biyu. (Bako)