in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kisan 'yan Habasha a Libiya
2015-04-21 10:48:54 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi tir da kisan 'yan Habashan nan da reshen kungiyar IS a kasar Libiya ya yi ikirarin aikatawa. Mr. Ban ya ce, hallaka mutane bisa dalilin biyayyarsu ga wani addini, mummunan aiki ne na rashin imani.

Ya ce, shirin da MDD ke marawa baya, na warware rikicin kasar Libiya shi ne mafi a'ala, wanda kuma ya dace dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar su runguma, domin kawo karshen halin da ake ciki a kasar. Mr. Ban ya jaddada cewa, ta hanyar hadin kan sassan kasar ne kadai 'yan kasar za su iya kaiwa ga cimma nasarar yaki da ayyukan ta'addanci.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kungiyar Daesh mai alaka da IS a Libiya ta fitar da wani faifan bidiyo ta yanar gizo, wanda ya nuna mayakanta na harbe, tare da fille kawunan wasu mutane wadanda kungiyar ta ce kiristoci ne 'yan kasar Habasha.

Faifan na kimanin mintuna 29, ya nuna yadda aka sare kan wasu mutane su kusan 12 a wani wuri kusa da wata gabar ruwa, sa'an nan aka nuna wasu kusan su 16 da aka harbe da bindiga.

Mayakan kungiyar ta Daesh dai sun bayyana rukunin farko na wadanda suka hallaka a matsayin makiyansu, wadanda ke tsare a gabashin kasar Libiya, yayin da kuma kaso na biyu mutane ne dake hannun dakarun kungiyar a yankin kudancin kasar ta Libiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China