in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 26 ne suka rasu a harin Sabongarin Zaria dake Najeriya
2015-07-08 14:01:09 cri

Rahotanni sun bayyana cewa, mutane 26 ne suka rasa rayukan su, sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai sakatariyar karamar hukumar Sabongari dake jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Shugaban asibitin koyarwa na Ahmadu Bello dake Zaria inda aka kai wadanda harin ya ritsa da su Lawal Khalid, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, ya zuwa jiya Talata, adadin wadanda aka tabbatar sun rasu sakamakon harin sun kai mutane 26.

Dr. Khalid, ya kara da cewa, baya ga wadanda suka rasu, akwai kuma wasu mutane 31 da suka jikkata, wadanda kuma ke samun kulawar jami'an jiyya a asibitin, ciki hadda mutum guda da ke cikin matsanancin yanayi.

Shugaban asibitin koyarwar ya kuma godewa al'ummar yankin bisa gudummawar jini da suke bayarwa, matakin da ya ce ya taimaka matuka wajen kubutar da rayukan wadanda ake jiyya.

Wata yarinya ce dai ta kai harin na kunar bakin wake, a lokacin da dandazon ma'aikatan jihar ke kokarin a tantance su, a harabar sakatariyar karamar hukumar ta Sabongari da hantsin ranar ta Talata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China