in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin tawagar UNSMIL
2015-03-06 10:35:07 cri

Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar UNSMIL a kasar Libiya, zuwa karshen watan Maris din nan. Hakan kuwa ya biyo bayan wani kuduri da wakilan kwamitin suka amince da shi a jiya Alhamis.

Rahotannin sun bayyana cewa, halin tsaro da Libiyan ke ciki, wanda ke barazana ga zaman lafiyar sauran kasashen duniya ne ya sanya kwamitin amincewa da tsawaita wa'adin aikin tawagar ta UNSMIL, har ya zuwa ranar 31 ga watan nan.

Kaza lika kwamitin ya amince da tsawaita dokar dakatar da cinikayyar danyan man kasar ba bisa ka'ida ba, tare da baiwa hukumomin da abun ya shafa, damar binciken jiragen ruwan dakon man kasar domin kaucewa karya wannan ka'ida.

Aikin tawagar ta UNSMIL dai ya hada da tallafawa gwamnatin kasar Libiyan, a kokarinta na tabbatar da wanzuwar tsarin dimokaradiyya, tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin shugaba Muammar al-Qadhafi a shekarar 2011 kawo wannan lokaci.

Yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa game da rikicin siyasar Libiyan a kasar Morocco karkashin inuwar MDD. Yayin da masu ruwa da tsaki ke fatan za a kai ga cimma matsaya guda, game da burin kafa gwamnatin hadaka ta rikon kwaryar kasar, tare da amincewa shirin tsagaita wuta, da wanzar da tsaro, da kuma batun kammala tsara daftarin kundin mulkin kasar bisa wani kaiyadajjen lokaci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China