Rundunar sojin Nigeriya a ranar Talatan nan ta kara jaddada kudurinta na ci gaba da yakin da yanzu haka take yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Marshal Alex Badeh ya tabbatar da hakan a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin kafuwar kawancen kungiyoyi masu zaman kansu.
Hafsan hafsoshin sojin ya fada wa bakin shi cewa, rundunar tsaron kasar tana kokari a wannan yakin da zai kara dinke kasar ta Nigeriya waje daya, ya tabbatar masu da cewa, kauyuka da dama da kungiyar ta hargitsa a baya, yanzu an dawo da su yadda suke, yana mai cewa, abin da rundunar tsaron take burin gani ke nan.
Marshal Alex Badeh daga nan sai ya ba da tabbacin cewa, babu wani aikin kawar da hankali da zai hana su yi wannan kokari na dawo da tsaro a kasar. (Fatimah)