in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Boko Haram sun kai hari kauyen Huyum dake jihar Bornon Najeriya
2015-06-10 10:29:51 cri

A kalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu, yayin wani farmaki da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a kauyen Huyum dake jihar Borno.

Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun aukawa kauyen ne a ranar Litinin, inda suka rika harbin mutane da bindigogi, lamarin da ya haddasa kisan wasu daga mazauna kauye, yayin da kuma da yawa suka tserewa gidajensu.

Rahotanni sun ce, maharan sun arce bayan aikata wannan ta'asa. A kuma jiya Talata ne wasu al'ummar yankin suka fara komawa domin gudanar jana'izar wadanda harin ya ritsa da su.

Wannan hari na baya bayan nan dai ya kara yawan mutanen dake barin gidajensu, sakamakon hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaddamarwa kan fararen hula, musamman a yankunan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China