Rahotannin daga garin Jos, babban birnin jihar Filato a Nigeriya na tabbatar da cewar, adadin wadanda suka mutu sanadiyar tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Lahadin nan ya karu zuwa 51 daga 44 tun da farko.
Mohammed Abdulsalam, jami'i mai kula da shiyyar arewa maso tsakiyar kasar na hukumar kula da ayyukan gaggawa na kasar wato NEMA ya sanar da karuwar adadin ga manema labarai a birnin Jos.
Ya ce, hukumar a ranar Litinin ta tabbatar da mutuwar mutane 44 a sanadiyar harin, kuma 67 na kwance a asibiti saboda raunuka daban daban da suka samu.
Abdulsalam ya ce, wadanda suka ji raunin dake kwance a asibitoci suna samun kula yadda ya kamata, sannan kuma kungiyar ba da agajin ta duniya wato Red Cross tana taimakawa da magunguna da sauran abun da za'a ciyar da mutanen. (Fatimah)