Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar DRC-Congo (MONUSCO) na ba da tallafi ga rundunar sojojin jamhuriyyar demokaradiyar Congo (FARDC) a yakin da take tare da 'yan tawayen FDLR na kasar Rwanda, in ji wakilin musammun na sakatare janar na MDD dake DRC-Congo, Martin Kobler.
Na je Beni tare da janar Etumba kafin kaddamar da ayyukan yaki da mayakan FDLR, ayyukan yaki da FDLR sun fara, a fagen daga ba a ganinsu da yawa har yanzu, in ji mista Kobler, tare da kara cewa, aiki ne da FARDC ke jagoranta amma tare taimakon MONUSCO ta fuskar dabarun yaki, tsare tsaren ayyuka, da kayayyaki. (Maman Ada)