in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta dauki matakin shawo kan cutar kwalara a Sudan ta Kudu
2014-05-28 12:07:09 cri

Ofishin MDD dake Sudan ta Kudu ya ba da rahoto cewar, adadin wadanda ake tsammanin sun kamu da cutar kwalara ta amai da zawo, a kasar ya karu zuwa 670, kuma wasu mutane 23 sun mutu, hakan ya sa MDD ta dauki matakin dakatar da yaduwar cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, yawancin wadanda ake tsammanin sun kamu da cutar suna babban birnin kasar Juba, to amma yanzu cutar na barazanar yaduwa zuwa wasu jihohi.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa wani taron manema labarai cewar, ruwan sama ya kusa faduwa, kuma matsalar ruwan dake taruwa wuri guda gami da magudanun ruwa da suka toshe da yawan jama'a ya mai da yankunan sun zama wuraren dake haifar da cututtuka da suka hada da kwalara.

Cutar kwalara ta barke a garin Juba, inda rikicin da aka yi watanni biyar ana yi tsakanin sojojin dake goyon bayan gwamnati da kuma wadanda ke adawa da gwamnati, ya haddasa dubannin jama'a rasa muhallansu, rikicin ya kuma haifar da dakatar da shigo da taimakon abinci da kuma kula da lafiyar jama'a.

A nata bangare, asusun yara ta MDD UNICEF ya yi nuni da bukatar da ake da ita ta taka rawar dukanin kasashe, tare da samar da karin kudade domin murkushe matsalar ta kwalara. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China