Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya bayyana a ranar Talata cewa, bai yi mamaki ba game da abkuwar tagwayen hare haren kunar bakin wake a birnin N'Djamena, hedkwatar kasar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 27, game da 'yan kunar bakin wake 4, da kuma jikkata mutane kusan dari, a cewar wani adadin wucin gadi da gwamnatin kasar ta ba da.
An sa ran cewa, wannan al'amari zai faru. Tun lokacin shirgarmu, musammun ma a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 2015, tare da kasashe makwabta da ke fuskantar barazanar ta'addanci. Na sha fadi ga gwamnati cewa, ta ci gaba tsaya wa cikin shirin ko ta kwana, ta sanya ido kan duk wasu abubuwan da ke kai da kawo a muhimman wurare da manyan gine ginen gwamnatin kasar, in ji shugaban Chadi bayan saukarsa daga cikin jirgin saman kasar da ya dauko sa daga Afrika ta Kudu, inda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 25. (Maman Ada)