in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun halaka a harin kunar bakin wake a jihar Yoben Najeriya
2015-07-06 10:18:22 cri

Rahotanni daga jihar Yobe a rewa maso gabashin Nigeriya na tabbatar da cewa, yanzu haka mutane 6 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani harin kunar bakin wake a wata mujami'a dake garin Potiskum.

Daga cikin wadanda suka mutu har da wanda ya kai harin, kamar yadda kakakin 'yan sanda jihar Toyin Gbadegesin ya yi bayani cewa, wani 'dan kunar bakin waken ya tada bam din dake nade a jikin shi a mujami'ar Redeem dake yankin Jigawa a garin na Potiskum wanda nan take ya hallaka mutane 5.

A cewar kakakin, wata mabiya a wannan mujami'a da ta samu rauni sanadiyar harin ta rasu, daga baya lokacin da ake ba ta jinya. Amma a cewar shim sauran wadanda suka samu rauni, suna samun jinya yadda ya kamata a dakunan shan magani daban daban a yankin.

Garin Potiskum dai ya fuskanci tagwayen harin kunar bakin wake a ranar 15 ga watan jiya wanda ya hallaka mutane 10, wadansu da dama kuma suka ji rauni.

Harin bam da ake kaddamarwa a kan jama'a fararen hula na daga cikin salon da 'yan ta'adda suka dauka don kawo rudani da tashin hankali da za su kara wa gwamnati matsin lamba.

An samu jerin hare-haren kunar bakin wake a wurare daban daban a kasar cikin wannan shekarar. Haka kuma kungiyar ta Boko Haram ta fadada harin kunar bakin wakenta zuwa kasashen Chadi da jamhuriyar Niger. Kasashen biyu yanzu haka tare da kasar Kamaru da ita kanta Nigeriya sun hada hannu waje daya na kafa rundunar sojin da za ta yaki da wannan kungiya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China