in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da 30 suka mutu a sabon harin arewacin Nigeriya
2015-07-06 09:39:19 cri

Rahotanni sun tabbatar da cewar, fiye da mutane 30 suka halaka a wani sabon harin 'yan ta'adda da wadansu masu dauke da makamai suka kai a birnin magaji dake jihar zamfara dake arewacin tarayyar Najeriya.

Kamar yadda shugaban karamar hukumar wajen Muhammad Gusami ya tabbatar da faruwan hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar ya ce, an kai harin ne a kauyukan Kokeya da Chigama.

Malam Muhammad Gusami ya ce, 'yan bindigar sun abkawa kauyen Kokeya ne da Babura, kuma suka kashe mutane biyu, tare da banka ma gidaje wuta, sannan suka yi awon gaba da dabbobi, galibi shanu.

Lokacin da ake cikin fargaban hakan kuma sai 'yan bindigar kashegari suka sake abka wa kauyen dake makwabtaka da na farko Chigama, inda suka kashe mutane sama da 30 wadanda har yanzu ake neman gawawwakinsu a cikin daji.

Shugaban karamar hukumar ya ce, gawawwakin da aka samo, an kai su babban asibitin birnin Magajin.

Haka kuma wannan labari, kakakin 'yan sanda na jihar Sanusi Amiru ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, sojoji da 'yan sanda sun isa kauyukan domin maido da doka da oda. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China