Ofisoshin hukumar lura da 'yan gudun hijra ta MDD UNHCR, da shirin abinci na WFP, sun bayyana bukatar neman taimakon kudade da yawan su ya kai dala miliyan 371, domin tallafawa dubban al'ummar Sudan ta Kudu dake gudun hijira a kasashe makwafta.
A cewar mai magana da yawun MDD Farhan Haq, tun barkewar rikicin kasar a tsakiyar watan Disambar bara ya zuwa yanzu, sama da mutane 204,000 ne suka tsere kasashen Sudan, da Uganda, da Habasha da kuma Kenya.
Farhan Haq ya ce, matsalar karancin tsaro, da rashin abinci a Sudan ta Kudun na iya kara yawan 'yan gudun hijirar, zuwa adadin da ka iya kaiwa 340,000 nan da karsehen shekarar da muke ciki.
Baya ga dubban al'ummar dake ficewa daga kasar, mai magana da yawun MDDr ya ce, akwai kuma wasu mutane sama da 700,000 a cikin kasar, da suka gujewa gidajensu. A sa'i daya kuma, kimanin mutane miliyan 3.7 ke fuskantar karancin abinci da tsaro.
Dauki ba dadin da ya barke a watan Disambar bara, tsakanin dakarun kabilar Dinka ta shugaba Salva Kiir, da 'yan kabilar Nuer masu biyayya ga korarren mataimakinsa Riek Machar, ya haifar da kisan fararen hula da dama.
Sai dai a wani ci gaban, bangarorin biyu sun amince da komawa teburin shawara a ranar Talata, da nufin gano bakin zaren matsalolin da suka dabaibaye kasar. Ana kuma sa ran tattaunawar da za su gudanar a birnin Addis Ababan kasar Habasha, za ta taimaka wajen cimma burin da aka sanya gaba.
Bugu da kari ofishin MDD mai kula da ayyukan ba da agajin jin kai, ya bayyana bukatar samar da karin kudaden tallafi, ga kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, domin fidda al'ummunsu daga mawuyacin halin da suke ciki.
Daraktan gudanarwar ofishin na OCHA John Ging ne ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin wani taron manema labaru da aka gudanar. Ging wanda ya kammala ziyarar aiki a kasashen biyu a 'yan kwanakin nan, ya ce, yankin Darfur na kasar Sudan, da sassan kasar Sudan ta Kudu da dama, na fuskantar karancin abinci, da matsanancin halin rashin tsaro. Lamarin da ya tilasawa hukumarsa, neman taimakon fidda su daga wannan hali. (Saminu)