Wakiliyar musamman ta sakatare janar na MDD dake kasar Sudan ta Kudu, madam Hilde Johnson ta kai ziyara a birnin Bentiu domin ganawa 'yan gudun hijirar da aka tsugunnar a wasu sansanonin da fararen hula ke samun kariya daga tawagar MDD dake tattare da mutane kusan dubu 45, in ji kakakin MDD Stephane Dujarric.
Madam Johnson ta bayyana cewa, jama'a na ganin ba a kiyaye tsaronsu, amma kuma suna zuwa hedkwatar tawagar UNMISS domin samun abinci, ganin cewa, babbar illar wadannan yake-yake ita ta rashin cimaka, in ji mista Dujarric a yayin wani taron manema labarai, tare da jaddada cewa, halin na cigaba da zuwa ko wace rana.
Madam Johnson da kuma ke jagorantar UNMISS, ta gana a ranar Talata da manyan jami'an jihar Unite domin tattauna game da wannan rikici, da kuma matsalar jin kai dake cigaba da tabarbarewa. Haka kuma jami'ar ta gana da ma'aikatan MDD dake wannan kasa, in ji kakakin. (Maman Ada)