in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 81 a arewacin Kamaru
2015-02-06 10:19:11 cri

Ministan tsaro na kasar Kamaru Edgar Alain Mebe ya tabbatar da cewa, 'yan tsageran Boko Haram sun kashe fararen hula 81 a wani hari da suka kai a yankin arewacin kasar ta Kamaru.

Ministan ya fada a cikin wata sanarwa cewar, alkalumman farko sun nuna cewar,mayakan Boko Haram sun kuma kashe sojojin Chadi 13 da kuma sojojin Kamaru guda 6.

Wata majiyar sojojin Kamaru ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, kimanin 'ya'yan kungiyar Islama ta Boko Haram kusan 700 dauke da muggan makamai daga Nigeria suka kaddamar da wani mummunan hari a kan garin Fotokol dake yankin nan mai nisa na arewacin Kamaru..

Majiyar sojojin ta bayyana cewar, an yi kazamin artabu tsakanin 'yan tsageran na Boko Haram da kuma dakarun hadin gwiwa na kasashen Chadi da Kamaru, a inda a tashin farko mayakan Boko Haram suka kwace garin har tsawon wasu awowi, to amma daga baya sai dakarun Chadi da Kamaru suka kaddamar da gumuzu tare da ceto garin daga hannun Boko Haram, hakan ya sa an kashe sojojin Boko-Haram a kalla 300. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China