Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, sun hallaka mutane 20 a kauyen Debiro na karamar hukumar Hawul dake jihar Borno, lokacin da suka farwa kauyen a ranar Litinin.
Shaidun gani da ido sun ce, 'yan bindigar dake kan babura da motoci, sun rika harbi kan mai-uwa-da-wabi, lamarin da ya janyo kisan mutane da dama, ciki hadda mata da kananan yara, baya ga wasu magidanta da suka yiwa yankan rago.
Kaza lika rahotanni sun ce, 'yan bindigar sun kone gidaje da dama, tare da wawashe dukiyoyin da amfanin gonar mazauna kauyen. Tuni dai wadanda suka tsira da rayukansu suka tsere zuwa kauyen Kworjafa mai nisan kilomita 250 daga birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno.
Lawal Usman wanda ya tsira daga farmakin, ya shaidawa majiyarmu cewa, ya zuwa ranar Talata, wasu daga al'ummar kauyen sun koma gida domin tantance irin asarar da suka yi.
Harin dai na kauyen Debiro ya auku ne kusan lokaci guda, da na wata kasuwa dake cikin birnin Maiduguri, inda tashin wasu tagwayen bama-bamai ya sabbaba kisan mutane a kalla 12. (Saminu)