in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane 2,000 ne suka nemi mafaka a Arewacin Darfur cikin mako guda
2014-04-08 10:18:32 cri

Hare-haren da aka kai kan wasu kauyukan dake Arewacin Darfur na kasar Sudan, sun tilastawa sama da mutane 2,000 neman mafaka a sansanin MDD dake yankin.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan, yayin taron manema labaru na rana-rana da yake gudanarwa. Haq ya ce, daga 1 ga watan nan na Afirilu kawo yau, daruruwan mutane mafiya yawansu mata da kananan yara, na ta tururuwa zuwa sansanin majalissar dake Mellit.

Ana dai zargin kungiyoyin tada kayar baya, ciki hadda ta "Rapid Support Forces" da kaddamar da hare-haren baya bayan nan kan kauyukan yankin. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar wanzar da zaman lafiya ta UNAMID, ke ci gaba da kokarin ba da kariya da tallafi ga sabbin 'yan gudun hijira a yankin, yankin da ke sham fama da sabbin tashe- tashen hankula, tun daga karshen watan Fabarairu.

Har wa yau, wasu rahotannin daga Khor Abeche, dake kudancin yankin na Darfur, na cewa, kimanin mutane 3,000, da fadace-fadace suka raba da gidajensu ne ke samun tallafi da mafaka a sansanin tawagar UNAMID dake yankin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China