Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewa, a kalla mutane 11 ne suka hallaka a ranar Litinin din nan a wasu hare-haren kunar bakin wake guda biyu a garin Potiskum, kamar yadda wata majiyar asibiti ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua.
Hare-haren dai ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram guda biyu ne suka kai su, wani a kan ofishin 'yan tsaro na saka kai da aka kafa domin kare mazauna daga irin wadannan hare-hare, sannan saura daya kuma a wata mashaya, in ji wani likita da ya nemi a sakaya sunan shi.
A kalla dai kuma mutane 8 sun samu raunuka suna karban magani, in ji likitan.
Potiskum, garin kasuwanci mafi girma a jihar Yobe ya taba samun hare hare da dama baya. (Fatimah)